‘Yan bindiga sun kashe mutum 5 a Kaduna – Kwamishina

‘Yan fashi. Hoto: BBC

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyar a kananan hukumomin Chikun da Igabi na jihar.

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

Aruwan ya bayyana cewa yan fashin sun kashe mutane biyu a karamar hukumar Chikun kuma sun lalata gine-gine biyu da suka hada da wurin bautar a yankin.

Kwamishinan ya ce sauran ukun an kashe su ne a yankin Lambar Zango da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a karamar hukumar Igabi.

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su sannan ya yi addu’ar Allah Ya ba mamacin hutu na har abada.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.