Mutane 70 sun ji rauni sakamakon fashewar tankar mai a Kano

Mutane 70 sun ji rauni sakamakon fashewar tankar mai a Kano

Wani mummunan bala’i ya faru, da yammacin Asabar, lokacin da wata tankar mai dauke da lita 6,600 na fetur ta kama da wuta, ta raunata mutane da yawa a yankin Sharade da ke cikin birnin Kano.

Hadarin ya faru ne lokacin da tankar mai lamba NSR 183 XW, ke sauke kayan mai a tashar Ihsan Petrol.

Guardian ta gano cewa tankar ta kama da wuta lokacin da igiyar wutar lantarki tsirara ta fado kan tankar a yayin da take sauke kayan.

Lamarin gobarar ya bar kusan mutane 70 tare da kuna yayin da zuwan hukumar kashe gobara ta ceci ranar. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sakataren kungiyar agaji ta Red Cross ta jihar Kano, Alhaji Musa Abdullahi, ya ce mazauna garin da kuma wasu mutane masu kwazo sun ceci mutane 70 da suka samu raunuka.

Ya bayyana cewa kafin zuwan aikin kashe gobara, kungiyar agaji ta Red Cross ta bayar da agajin gaggawa ga mutane da dama yayin da wadanda suka samu munanan raunuka aka kaisu asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin kula da lafiyarsu.

A yayin haka kuma, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa mutane 64 sun samu rauni a lamarin.
A cewarsa, ma’aikacin ya samu kira daga wani Malam Shaubu Umar da misalin karfe 4.24 na yamma game da abin da ya faru da gobarar kuma mutanen ofishin suka zo ‘yan mintoci kaɗan don kashe wutar.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.