Yarinya ‘yar kwana ɗaya ta mutu cikin rijiya

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, an tsinci gawar wata jaririya wacce ake zargin tana da kwana daya a wata rijiya da ke kauyen Tsalle a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Lamarin, wanda ya faru a ranar Alhamis, an tabbatar da shi a cikin wata sanarwa daga Alhaji Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano.

Abdullahi ya ce an samu kiran wayar ne da misalin karfe 12:25 na ranar Alhamis daga wani Abubakar Ahmed-Dandago.

“Da samun labarin, muka hanzarta tura jami’anmu na ceto zuwa wurin da misalin karfe 12:43 na rana,” in ji Abdullahi.

Ya ce an fito da yarinyar daga cikin rijiyar ta mutu.

Abdullahi ya ce an mika gawar ga ofishin ‘yan sanda na shiyyar Gezawa, don ci gaba da bincike.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa, har yanzu ba a san asalin yaron ba, musamman iyayenta yayin da abin da aka fara zargi shi ne an jefa jaririn a cikin rijiyar, ya mutu tuni.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.