‘Yan bindiga sun kai hari Kwalejin Fasaha a jihar Kaduna, sun yi awon gaba da malamai,’ yan uwa

Wasu ‘yan bindiga a ranar Alhamis sun kai hari kan Nuhu Bamalli Polytechnic, Zaria, a jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu malamai da iyalansu.

Wani jami’in hukumar kula da ayyukan sintiri na Kaduna wanda ya yi magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) amma ba ya son a ambaci sunansa, ya ce wasu daliban makarantar ma sun jikkata.

Jami’in, wanda bai ba da cikakken bayani ba, ya ce lamarin ya faru ne a daren Alhamis tsakanin 10:30 na dare zuwa 11 na dare.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na makarantar, Malam Abdullahi Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa jami’an hukumar na kokarin gano ainihin adadin mutanen da lamarin ya shafa.

Hakazalika, ASP. Mohammed Jalige, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, reshen jihar Kaduna, shi ma ya tabbatar wa da faruwar lamarin, amma ya ce har yanzu yana jiran cikakken bayani kan lamarin.

Ya yi alkawarin tuntubar manema labarai da zaran an samu irin wadannan bayanai.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.