Buhari ya nada Ilelah a matsayin Darakta-Janar na NBC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Balarabe Ilelah, wani gogaggen mai yada labarai a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Kasa (NBC).

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya sanar da nadin a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Juma’a.

Ya ce nadin Mista Ilelah ya kasance na tsawon shekaru biyar a matakin farko.

Segun Adeyemi, mai taimakawa na musamman ga shugaban kasa (Media), ofishin Ministan Yada Labarai da Al’adu ne ya sanya hannu a sanarwar.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.