Buhari Ya Nada Ilelah a Matsayin Darakta-Janar na NBC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani gogaggen mai yada labarai Balarabe Shehu Ilelah a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Watsa Labarai ta Kasa (NBC).

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed wanda ya sanar da nadin a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a a Abuja, ya ce nadin Ilelah na tsawan shekaru biyar ne a matakin farko.

Ya karbi aikin ne daga hannun Prof Armstrong Idachaba wanda aka nada shi kan mukamin na rikon kwarya tun daga watan Fabrairun 2020 bayan dakatar da Mallam Is’haq Modibbo Kawu

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.