Lalong ya ƙaddamar da ayyuka don bikin cika shekaru 6 a ofis

Lalong Hoto / TWITTER / PLSGOV

Baya ga kaddamar da ayyukan a ranar Juma’a a Jos, gwamnan ya kuma aza harsashi na wasu sababbi kuma ya duba ayyukan da ake gudanarwa.

Da yake jawabi a takaice a wurare daban-daban na aikin, gwamnan ya bayyana kudurin gwamnatinsa na isar da romon dimokiradiyya ga mutane

Ya ce zai ci gaba da fara ayyukan da za su shafi rayuwar jama’a kai tsaye.

Lalong ya kuma yi alkawarin kara himma da kirkirar manufofi da shirye-shirye wadanda za su kawo dawwamammen zaman lafiya a jihar.

Ya yi kira ga mutane da su ba shi goyon baya tare da ba shi hadin kai a kokarinsa na tabbatar da ci gaban jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wasu daga cikin ayyukan da aka kaddamar sun hada da hanyoyi, cibiyoyin sarrafa ruwan sha, da gonaki, da sauransu.

Ayyukan da aka kaddamar da kuma duba su duka suna cikin Jos ta Arewa da kananan hukumomin Jos ta Kudu na jihar.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.