Wata mummunar cuta ta kashe mutane 6 a Kano – Jami’i

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa

Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Aminu Ibrahim-Tsanyawa, wanda ya tabbatar da hakan ya ce an kwantar da wasu mutane 46 da cutar ta shafa.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce cutar ta bulla a kauyen Gandun Koya a ranar 7 ga watan Mayu, kuma ta bazu zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ita.

“Dalilin barkewar cutar ana iya alakanta shi da bude ido da kuma rashin tsabtace muhalli a cikin al’umma.

“Marasa lafiyar sun gabatar da alamun gudawa da amai.

“Mutane shida ne suka mutu sakamakon cutar, an sallami 28 sannan wasu 18 na kan karbar magani,” in ji shi.

Ibrahim-Tsanyawa ya ce ma’aikatar ta fara bincike don gano musabbabin cutar.

Yayin da yake sake nanata kudirin gwamnatin jihar na wayar da kan jama’a da kuma hanyoyin kariya, Ibrahim-Tsanyawa, ya bukaci mutane da su kiyaye tsabtace muhalli da kuma kiyaye tsabtar kansu don magance cutar.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.