Mutane 64 sun ji rauni sakamakon fashewar tankar mai a Kano

Mutane 64 sun ji rauni sakamakon fashewar tankar mai a Kano

[FILES] Jihar kano. Hotuna: YOUTUBE

Lamarin ya faru ne a gidan mai na Al-ihsan da ke Sharada a cikin karamar hukumar Municipal ta Kano.

Malam Saminu Abdullahi, kakakin hukumar kashe gobara ta Kano, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kano.
Abdullahi ya ce daga cikin wadanda suka jikkata, ma’aikatan hukumar kashe gobara su takwas sun shiga hannu, ya kara da cewa ba a rasa rai ba.

“Da samun kiran waya daga wani Malam Umar Shuai’bu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da misalin karfe 04:20 na rana cewa akwai tankar da ta kama da wuta a Sharada.

“Mun hanzarta tura ma’aikatanmu da motocinmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 04:24 na yamma don ceton wadanda abin ya shafa”.
Ya ce tankar tana sauke kayan mai a gidan mai lokacin da lamarin ya faru.

“An kai wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammed da kuma asibitin Nassarawa,” in ji shi.

Ya yi kira ga jama’a da su ringa kiran hukumar kashe gobara nan take da zarar sun gamu da duk wata matsala ta gobara.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.