Ganduje ya jajantawa tsohon gwamnan Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa

Ganduje ya jajantawa tsohon gwamnan Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa

By Abba Dukawa


Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya jajantawa gwamnan farar hula na farko na jihar Jigawa, Alhaji Ali Sa’ad Birnin Kudu bisa rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Hafsat wacce ta rasu kwanan nan bayan fama da rashin lafiya.

Late Hajiya Hafsat Sa’ad Birnin Kudu aged 83 left behind seven children and 63 grandchildren.

A cikin sakon nasa, Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a wajen jana’izar marigayin wanda ya gudana a Masallacin Umar Ibn Khattab ya mika ta’aziyar sa ga iyalai, gwamnati da jama’ar Jihar Jigawa.

“Allah Ya ba ku da iyalanku baki daya karfin gwiwa da juriyar wannan babban rashi. Gwamnati da mutanen jihar Kano suma suna cikin bakin cikinku yace ”.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.