Jirgin kasa dauke da bututun ruwa ya kauce hanya a Kaduna

Jirgin kasa dauke da bututun ruwa ya kauce hanya a Kaduna

Wani jirgin kasa dauke da bututun ruwa daga Legas zuwa Zariya ya kauce hanya a Kaduna, kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.

NAN ta tattaro cewa babu wanda ya ji rauni a hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 5:50 na yammacin ranar Asabar a kusa da Unguwar Kanawa, daura da Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya shaida wa NAN cewa, “Ba a samu asarar rai ba kuma ba a samu asarar dukiya ba”.

“Jirgin kasan ya bunkasa wasu yan fage kuma ya kauce hanya, yana kan hanya ne daga Legas zuwa Zariya.

Jalige ya kara da cewa “Mun tura jami’anmu don su tsare wurin da kuma kare bututun,”

Shima kwamandan hukumar kiyaye haddura na jihar Kaduna, Hafiz Mohammed, ya bayyana hatsarin a matsayin karami.

“Jirgin locomotive din (shugaban) ya kauce yayin da yake tsaye, koci daya kuma ya kauce, yayin da koci biyar suka kife.

“Wasu bututun sun watse saboda hatsarin. Koyaya, an tura rundunonin sintiri na ‘Operation Yaki’ don aikin tsaro a yankin.

“Ba a rasa rai ba kuma ba wanda ya samu rauni.

“An tuntubi Hedikwatar Railway don aika tawagarsu ta fasaha zuwa wurin,” in ji Mohammed.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.