Masarautar Katsina ta tsige Hakimin ta saboda taimakawa ‘yan ta’adda

A ranar Asabar din da ta gabata ne masarautar ta Katsina ta sanar da korar “Sarkin-Pauwan Katsina” da Hakimin Kankara, Alhaji Yusuf Lawal, bisa zarginsa da hannu wajen taimakawa ‘yan bindiga a yankinsa.

Alhaji Bello Mamman-Ifo, Sakataren Majalisar ya bayyana hakan ta bakin jami’in yada labarai na masarautar, Alhaji Ibrahim Bindawa, a Katsina.

Mamman ya ce korar Lawal a matsayin hakimi zai fara aiki nan take.

Ya ce binciken da aka gudanar kan zargin da ake yi wa Lawal cewa yana taimakawa da kuma tayar da kayar baya a yankinsa ya nuna cewa ya aikata laifin.

“Binciken ya same shi da laifin duk tuhumar da ake yi masa.

“An tura rahoton zuwa ga gwamnatin jihar kuma an yi umurni da a kore shi daga Hakimin,” in ji shi.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.