Majalisar Kaduna ta dakatar da ‘yan majalisa uku, ta ce kujerar tsohon kakakin ba kowa

Majalisar Kaduna ta dakatar da ‘yan majalisa uku, ta ce kujerar tsohon kakakin ba kowa

Yayin da rikici ya dabaibaye majalisar dokokin jihar Kaduna, a jiya, ‘yan majalisar sun kara wa’adin dakatar da mambobinta uku.

Wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan na Shugaban Majalisar, Haruna Sambo, ya bayyana cewa an tsawaita dakatarwar da suka yi da watanni 12.

A cewarsa, an yanke shawarar ne yayin zaman majalisar wanda Mataimakin Shugaban, Isaac Auta ya jagoranta jiya.

“Majalisar ta kara wa’adin dakatar da mambobin uku tare da bayar da dakatarwar ga wani, Salisu Isa, mai wakiltar Magajin Gari,” in ji shi.

Sanarwar ta zayyana Mukhtar Hazo da Nuhu Shadalafiya, dukkansu tsaffin mataimakan kakakin majalisar, da kuma Yusuf Liman a matsayin wadanda za su sake dakatar da wasu watanni 12.

Amma, ta bayyana kujerar tsohon kakakin, Aminu Shagali, babu kowa.

Majalisar ta ce irin wannan matakin ya zama wajibi biyo bayan rashin halartar tsohon kakakin na tsawon lokaci daga majalisar mai tsarki.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.