Bagudu ya yi wa Sultan ta’aziyyar rasuwar babban wansa

Bagudu ya yi wa Sultan ta’aziyyar rasuwar babban wansa

Daga Umar D. Ado, Sokoto

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya yi ta’aziyya ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III game da rasuwar babban wansa, Chiroman Sakkwato, Alhaji Buhari Abubakar, wanda ya rasu a ranar Alhamis din da ta gabata, bayan fama da rashin lafiya.

Yayin da yake fadar mai martaba Sarkin, Gwamnan ya bayyana mutuwar Chiroma a matsayin babban rashi ga jihohin Sakkwato da Kebbi, yana mai rokon Allah Madaukakin Sarki da Ya ba marigayiyar Aljannat Firdaus da dangin babban karfin da za su iya jure wannan babban rashi.

”Mun ji rashin sa’ar rashin Chiroman Sokoto, shi ya sa muke nan a yau, a ziyarar ta’aziyya da kuma yi wa marigayin addu’a.

“Rashin dai na dukkanin mu ne, babbar asara ce ga Jihohin Sakkwato da Kebbi,” in ji shi.

Gwamnan, yayin da yake nuna bakin ciki game da mutuwar Chiroma, ya kuma roki Allah da ya ba Sultan karfin gwiwar jure rashin.

A nasa martanin, Sarkin Musulmi ya nuna godiya ga Gwamnan bisa ziyarar ta’aziyyar.

Sarkin Musulmin, yayin da yake jin daɗin dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin jihohin biyu, ya yi addu’ar Allah ya saka da alheran sa na watan Ramadana ya kuma sakawa gwamnan da ziyarar.

Marigayi Chiroma yana da shekaru 64, ya bar mata biyu da yara da yawa.

Ya mutu a daren ranar Alhamis din da ta gabata, yayin da aka yi sallar Jana’iza a ranar Juma’a.

Hakazalika, Gwamna Bagudu ya kasance a yankin Kanwuri don yi wa dangin marigayi Hajiya Aisha Ahmadu Bello, diyar marigayi Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ta’aziyya.

Marigayi Hajiya Aisha ta rasu ne a ranar Juma’ar da ta gabata bayan fama da rashin lafiya.

Marigayin matar marigayi Marafa Danbaba ne, haka kuma mahaifiya ga Alhaji Hassan Ahmad Dan Baba, Magajin Garin Sokoto.

Gwamnan na Kebbi tare da mukarrabansa sun yi addu’ar Allah ya yiwa mamacin rahama tare da iyalensa, jurewar jure rashin

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.