Rashin tsaro: KNSG ta rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda

Rashin tsaro: KNSG ta rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda

Daga Nasiru Muhammad

Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda ba tare da bata lokaci ba

Rufe kwalejin wanda Kwamishinan Ilimi na jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya sanar ya zama tilas biyo bayan wani rahoton tsaro da ya tayar da hankali da kuma bukatar kare rayukan dalibai, malamai da sauran ma’aikatan kwalejin.

A wata sanarwa da Babban Jami’in Hulda da Jama’a, Aliyu Yusuf ya fitar kuma ya bayyana wa The Triumph ya ce kwamishinan ya bukaci iyaye da su gaggauta kwashe ‘ya’yansu daga kwalejin kuma su jira karin umarnin.

Kwamishinan ya ci gaba da amfani da wannan dama wajen bayyana godiyar gwamnatin jihar ga iyaye da masu kula da su bisa ga mara baya goyon baya da hadin kai kan manufofin gwamnati da umarnin ta musamman kan al’amuran da suka shafi tsaro.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.