Sarkin Taraba ya ba makiyaya wa’adin kwanaki 30 su bar dazuzzuka


Sarkin masarautar Muri a jihar Taraba, Abbas Tafida, ya bayar da wa’adin kwanaki 30 ga makiyaya da ke tsoratar da mazauna jihar kan barin dazuzzuka a cikin jihar ko kuma tilasta musu yin hakan. Sarkin ya bayar da wa’adin ne a ranar Talata bayan sallar Idi.

Wannan ya biyo bayan yawaitar sace-sacen mutane, kashe-kashe, da hare-hare a jihar da wasu miyagu da ake zargin makiyaya ne. Ya yi ikirarin cewa Fulani makiyaya ne ke da alhakin aikata laifi a jihar don haka ya kamata su bar dazuzzukan da ke cikin jihar cikin kwanaki 30 ko kuma a tilasta musu fita.

Sarkin, wanda ya yi magana da harshen Hausa, ya bukaci shugabannin Fulani makiyaya da su fitar da miyagun kwai a tsakanin su.

“Fulaninmu makiyaya a cikin dazuzzuka, kun shigo wannan jihar ne kuma mun karbe ku, me ya sa za ku zo garuruwa da kauyuka don sace mazauna, ko da kuwa har ya kai ga fyade ga matanmu?

“Saboda wannan barazanar da ba ta karewa, an ba kowane Bafulatani makiyayi a cikin wannan kwanaki 30 wa’adin barin daji. Mun gaji da rashin bacci ba dare ba rana kuma yunwa kadai a cikin kasa tana da girma kuma ba za mu bari ta ci gaba ba, ”in ji Sarkin.

Taraba, da ke arewa maso gabashin kasar, na fuskantar munanan laifuka tun daga satar mutane zuwa hare-haren ‘yan fashi.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.