Zulum Ya Kaddamar Da Indimi, Sauran A Matsayin Majalisar Gudanarwar Jami’ar Borno

Zulum Ya Kaddamar Da Indimi, Sauran A Matsayin Majalisar Gudanarwar Jami’ar Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kaddamar da majalisar zartarwar jami’ar jihar.

Gwamna Zulum ne ya jagoranci bikin kaddamarwar wanda aka gudanar a ranar Litinin a dakin taro na gidan gwamnatin jihar, Maiduguri.

Majalisar gudanarwa tana karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaban kamfanin Oriental Energy Resources Ltd, Alhaji Mohammed Indimi a matsayin Shugaban kuma Pro-Chancellor na Jami’ar Borno.

Sauran mambobin sune; Farfesa Abubakar Mustapha, Farfesa Bankole Ogumbameru, Farfesa Shettima Umara Bulakarima, Alhaji Lawan Buba, wakilin majalisar dattijai na jami’ar, wakilin taron jama’ar jami’ar, ma’aikatar manyan makarantu yayin da rajistar jami’ar ke zama Sakatariyar Majalisar.

Ya umarci majalisar da ta tsara manufofi da nufin tabbatar da inganci da kuma kula da karancin kayan aiki cikin tsanaki.

Zulum ya kuma yi kira ga majalisar da ta inganta hadin gwiwa da sauran Jami’o’in don bunkasa kamfanoni da hadin gwiwa a bangaren koyarwa da bincike da suka dace don daukaka Jami’ar Jihar Borno.

Gwamnan ya tabbatar wa majalisar kudurinsa na samar da duk wani taimako da goyon bayan da Jami’ar ke bukata lokaci zuwa lokaci.

Zulum ya yi kira ga shuwagabannin da su inganta da’a da nuna gaskiya da kuma sanya key a cikin tsarin sauye-sauye na gwamnati ta hanyar tsarin ci gaban shekaru 25 da kuma shirin sauya fasalin shekaru 10.

Ya kuma kara da jan hankalin mahukuntan jami’ar da su tinkaho da irin kwarewar da Alhaji Indimi ya samu don bunkasa wannan jami’ar da shekara daya. Ya ce amincin Indimi da jajircewarsa ba a cikin shakku ko kadan.

Gwamnan tare da shuwagabannin da mambobin majalisar gudanarwar sun zagaya jami’ar jihar Borno.

Posted on

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.