‘Yan bindiga sun kashe mutane 4, sun jikkata 1 a Kaduna – Kwamishina

‘Yan bindiga HOTO: Shutterstock

Kwamishinan Tsaro na Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan, ya sanar da wannan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Aruwan ya ce hukumomin tsaro sun ba da rahoton harin a kan Goska da ke karamar hukumar Jema’a na jihar.
Ya ce ‘yan fashin sun mamaye yankin suka kashe mutane hudu.

“Biyu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su maharan sun kashe su a gonakinsu; mace daya ta samu rauni daga harbi kuma an garzaya da ita asibiti, ”inji shi.

Kwamishinan ya kuma ce Gwamna Nasir el’Rufai ya nuna bakin ciki kan rahotannin sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan rayukan mazauna garin da ‘yan ta’addan suka kashe.

Gwamnan ya aike da ta’aziyya ga iyalansu tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.

Aruwan ya ce ana ci gaba da yin sintiri a yankin baki daya, tare da bincike kan harin.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.