‘Yan bindiga sun kashe mutum hudu, sun ji wa daya rauni a kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a Goska, jihar Kaduna, kamar yadda kwamishanan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana.

A cewar kwamishinan, kwarton da aka kashe sun hada da Wakili Kon, Yusuf Joshua, Martha Ayuba da Lami Peter

“Wakili Kon da Yusuf Joshua maharan sun far musu kuma sun kashe su a gonakinsu. Wata mata, Laraba Silas, ta samu raunuka daga harbin bindiga sannan aka garzaya da ita asibiti, ”in ji Aruwan.

“Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna bakin ciki game da rahotannin, sannan ya yi addu’ar Allah ya jikan rayukan mazauna garin da‘ yan fashin suka kashe. Gwamnan ya aike da ta’aziyya ga danginsu, tare da yi wa dan kasa da ya jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa. ”

Aruwan ya ce ana ci gaba da sintirin tsaro a yankunan, tare da bincike kan harin.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.