Sojoji sun kashe yan bindiga 3 a jihar Sokoto


Daga Chuks Oyema-Aziken

Sojojin Najeriya da ke aiki a kusa da garin Sabo Birni da ke kan iyaka da Jihar Sakkwato sun kashe ‘yan bindiga 3 tare da kwato makamai a ranar 1 ga Yuni 2021.

Mai magana da yawun rundunar, Birgediya Janar Mohammed Yerima a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ya ce an yi hakan ne bayan samun sahihan bayanai na ‘yan bindigar da ke dauke da makamai a kafa daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya da misalin karfe 11 na dare.

“Sojojin da ke sa ido sosai sun yi nasarar kwanton-bauna a kan hanyar da ake zargi kusa da Garin Naimaimai kuma suka kashe maharan 3. Kayayyakin da aka kwato sun hada da bama-bamai na RPG da caja na RPG, bindigar mashin, bindigar AK47 da sauran kayan hadawa da kuma wasu nau’ikan alburusai daban-daban.

“Shugaban hafsan sojan kasa Manjo Janar Faruk Yahaya ya yabawa kokarin da sojojin suka yi sannan ya bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu a mamayar duk wasu haramtattun hanyoyi da ke kewaye da yankunan kan iyaka da Jamhuriyar Nijar don dakile duk wani motsi na makamai da alburusai zuwa cikin kasar.”

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.