Bello ya ziyarci Buhari, yayi alkawarin tabbatar da tsaro

Gwamna Yahaya Bello da Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Kasa, Abuja. Hoto / TWITTER / NIGERIAGOV

Bello ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da suka yi da Buhari.

Gwamnan ya kuma yaba wa Buhari kan kokarin da yake yi na dorewar hadin kan kasar.

“Ina amfani da wannan damar don in yaba wa Shugaban kasar kan irin abubuwan da ya ke yi wa kasar nan da kuma yadda ya sa muka hada kai.

“Na tabbatar wa Shugaban Kasa na ci gaba da ba da goyon baya don ganin cewa Jihar Kogi kasancewarta mashigar tsakanin Arewa da Kudu ta ci gaba da tsayawa tare da tabbatar da cewa cibiyar ta ci gaba da rikewa.

“Shugaban kasar yana matukar farin ciki da nasarorin da muka samu a jihar ta Kogi ya zuwa yanzu kuma ya bukace mu da mu ci gaba da yin hakan.”

Bello ya ce zai ba da “amsa mai gamsarwa” ga wadanda ke kiran sa ya tsaya takarar shugaban kasa idan lokaci ya yi.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Bello ya samu ci gaba matuka wajen dakile rashin tsaro a Kogi, lamarin da ya jawo masa farin jini a cikin kasa da ma duniya baki daya.

Author: Arewa Republik

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.